IMF na goyon bayan yaki da rashawa a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Misis Lagarde ta yabawa Shugaba Buhari a kan ayyukan da yake yi domin ci gaban Najeriya.

Shugabar Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, Christine Lagarde ta ce hukumarta na goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a Najeriya.

Misis Lagarde ta bayyana haka ne a fadar shugaban Najeriya a wata ziyara da take yi a kasar.

Shugabar ta IMF ta ce, "Ina so na bayyana karara cewa ban zo nan domin na nemi kasarku ta karbi bashi ba."

Misis Lagarde ta kara da cewa, "A gaskiya Najeriya ba ta bukatar karbar bashi ganin yadda shugaban kasa da jami'an gwamnatinsa suka jajirce wajen kawo ci gaban kasar".

Shugabar IMF din ta ce ba batun bai wa Najeriya bashi ne ya kai ta kasar ba.

Najeriya dai na fama da matsanancin rashin kudi sakamakon faduwar farashin man fetur a duniya da kuma zargin sace kudin da ake yi wa jami'an tsohuwar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, lamarin da wasu ke ganin zai sa kasar ta ranci kudi domin aiwatar da ayyukan ci gaba.