An tilasta wa mata saka kallabi a Gambia

Hakkin mallakar hoto AFO
Image caption Shugaba Jammeh da matarsa Zeinab

Gwamnatin kasar Gambia ta haramta wa ma'aikata mata barin kawunansu babu dan-kwali a wuraren aiki.

Wata wasikar sirri da ta fito daga wajen gwamnatin, wacce aka kwarmatawa wata jarida mai zaman kanta, ta bayyana cewa "Dole ne mata ma'aikata su rika daura dan-kwali ta yadda zai rufe kawunansu sosai", ko da ya ke ba a bayyana dalillin yin hakan ba.

A watan jiya ne Shugaba Yahya Jammeh ya ayyana kasar a matsayin mai bin tafarkin Musulinci.

Ya kara da cewa ba za a tursasa wa kowa kan irin tufafin da zai rika sanyawa ba, kuma mabiya sauran addinai za su iya ci gaba da yinsa ba tare da tsangwama ba.

Kasar ta Gambia ta yi fice saboda masu yawon bude ido daga yammacin duniya na kai ziyara a bakin tekunanta.

A shekarar 2013 ne Mista Jammeh ya janye kasarsa daga cikin kungiyar kasashen Commonwealth, yana mai bayyana ta da cewa kungiya ce ta 'yan mulkin-mallaka.