Ana ta da jijiyoyin wuya kan zaben Ghana

Image caption ghana masu zabe

A kasar Ghana, ana ta da jijiyoyin wuya tsakanin jam'iyyun siyasar kasar kan shawarar da hukumar zaben kasar ta yanke cewa ba za ta sake shirya wata sabuwar rijistar masu zabe kafin a gudanar da babban zaben kasar a cikin wannan shekarar ba.

Hukuman zaben dai ta ce wani kwamiti da ta kafa don duba lamarin ya ba ta shawarar cewa sake yin rijistar ba shi da wani amfani.

Jam'iyyun siyasar kasar na cewa baki da dama ne da kuma yara da shekarun su ba su kai zabe aka yiwa rejistar yin zaben.

'Yan hamayya da jam'iyar da ke mulki sun bayyana ra'ayoyi daban-daban kan lamarin.