Bishiyoyi na rage gurbatar yanayi

Hakkin mallakar hoto thangarajkumaravel
Image caption kurmi

Bishiyoyi na iya taimakawa wajen rage hayaki mai gurbata muhalli kamar yanda wani bincike da aka gudanar a Ingila ya nuna.

Wannan tsari na taimaka wa bangaren noma wajen rage yawan hayaki mai gurbata muhali da kashi 80 cikin 100 zuwa shekara ta 2050 kamar yanda binciken ya gano.

A Ingila dai kashi 9 cikin 100 na hayaki da ke gurbata muhalli na fitowa daga bangaren ayyukan noma.

To sai dai binciken ya nuna cewa kara yawan bishiyoyi zai kara bunkasa albarkar filayen noma da kiwo.

Masu binciken sun kara bayyana cewa idan aka kara dasa itatuwa a cikin filayen da ba a noma a ciki, bishiyoyi za su karu daga kashi 13 cikin 100 zuwa kashi 30 cikin 100 zuwa tsakiyar wannan karni, kuma a ceto filin noman da zai kai kadada dubu 700 daga salwanta.

Wannan kuma zai sa bangaren noma ya taimaka wajen rage gurbatacciyar iska da kashi 80 cikin 100 daga 1990 zuwa 2050.