An bukaci Nijar ta gyara kundin zabe

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar kasashen rainon Faransa ta ce kundun rijistar yin zaben Jamhuriyar Nijar ya na da ingancin da zai sa a yi zaben watan Fabriaru idan har aka yi wasu 'yan gyare gyare a cikinsa.

Sauye-sauyen sun hada da kawar da rumfunan zabe 300 na boge da kuma katunan zabe 25,000 wadanda aka yi su sau biyu.

Shugaba Mahamadou Issoufou zai tsaya takara a karo na biyu kuma ana sa ran zai ci zaben, sai dai masu suka sun ce a kullum yana kara kasancewa mai mulkin kama-karya kuma yana murkushe 'yan hammaya kafin ma zaben.

A watan Disambar da ya wuce ne dai 'yan hamayya suka yi watsi da rijistar jerin sunayen wadanda suka cancanta su kada kuri'u, inda suke cewa tsarin zaben bai cika bukatunsu ba.