Nijar: Mun kusa murkushe Boko Haram — Sojoji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption niger shugaban kasa da ministan tsaro

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun ce suna samun nasara a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Babban Hafsan sojin kasar, Janar Seini Garba ne ya bayyana haka inda ya ce nan ba da jimawa ba za su murkushe Boko Haram a kasar.

Janar din ya yi bayanin ne a lokacin da yake yi wa shugaban kasar Mahamadou Issoufou barka da sabuwar shekarar 2016.

A nasu bangaren wasu mazauna yankin Diffa, jahar da ta fi fama da matsalar ta Boko Haram, sun bayyana gamsuwarsu dangane da zaman lafiyar da ake samu a yankin sakamakon fatattakar mayakan Boko Haram da sojojin Nijar din suka yi.