Mahara sun kona motar safa a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ministan Tsaron Saudiyya Muhammad Bin Salman

Rohotanni daga Saudiyya na cewa wasu mutane dauke da makamai sun banka wa wata motar-safa wuta, wadda ke dauke da ma'aikata za ta kai su wuraren aiki a lardin gabashin kasar.

Kafafen yada labaran kasar dai sun ce babu wanda ya jikkata, haka kuma ba a san wanda ya kai harin ba.

Kodayake an kai harin ne a lokacin da ake zaman dar-dar-dar a yankin, bayan hukuncin kisan da aka zartar wa wani fitattcen Malamin Shi'a, Nimr Al Nimr, wanda aka zarga da aikata ta'addanci.

Malamin dai ya yi rayuwarsa ne a lardin gabashin kasar, inda yake wa'azi, kuma lardin wuri ne da mabiya akidar Shi'a suka yi kaka-gida, wadanda kuma ke jin cewa mabiya akidar sunni da ke da rinjaye a kasar Saudiyyar na maida su saniyar-ware