Majalisar dinkin duniya ta yi tir da Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai majalisar dinkin duniyar ba ta ce komai a kan kisan da Saudiyya ta yi wa malamin Shi`ar nan ba.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi tir da harin da masu zanga-zanga suka kai kan ofishin jakadancin Saudiyya da ke Iran, lamarin da ya yi sanadin yanke huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

Kwamitin ya bukaci Iran ta dinga kare martabar ofisoshin jakadanci.

Sai dai kwamitin bai ce komai a kan hukuncin kisan da Saudiyyar ta yi wa malamin Shi'ar nan Nimr Al-Nimr ba.

Kasar Saudiyyar dai ta ce sabanin da ke tsakanin ta da Iran ba zai shafi kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a yankinsu ba.

Jakadan Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya, Abdallah Al-Mu'allimi, ya ce kasarsa za ta kara himma wajen dawwama zaman lafiya a kasar Yemen da Syria.

Ya ce, "A namu bangaren ba zai shafe mu ba, saboda za mu ci gaba da sa-himma wajen goyon bayan duk wani kokari na wanzar da zaman lafiya a Syria da Yemen da duk inda ake bukatar hakan".

Jakadan ya ce za a iya magance rikicin ne idan Iran ta daina yin shisshigi ga al'amuran da suka shafi wasu kasashe.