IMF ya soki tsarin babban bankin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Bukola Saraki Twitter
Image caption Lagarde ta soki CBN a ganawarta da Saraki

Shugabar asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, Christiane Lagarde ta ce asusun ba ya goyon bayan matakin takaita amfani da kudaden kasashen waje a Najeriya.

Hakan na daga cikin matakan da gwamnatin kasar ta dauka domin kara wa kudin kasar wato Naira karfi.

Misis Lagarde din wadda ta fadi haka a ganawarta da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ta kara da cewar ya kamata kasar ta cire tallafin man fetir.

Lagarde din ta kuma shawarci Najeriya da ta rage darajar kudin kasar tare da kara yawan harajin da ake dora wa a kan kayayyaki.

A cewar shugabar IMF din Najeriya na daya daga cikin kasashe masu karancin haraji a kan kayayyakin a daukacin nahiyar Afirka.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Tare da manyan jami'an gwamnatin Nigeria
Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Lagarde ta jinjina wa Buhari a fadar Aso Rock

Masu sharhi na kallon kalaman Lagarde a matsayin tufka da warwara kan batun cewa asusun ya gamsu da duk tsare-tsaren da shugaba Buhari ya dauka.