Jami'an diplomasiyyar Iran sun koma gida

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Shi'a sun tir da kashe Sheikh Nimr

Jami'an diplomasiyyar kasar Iran a Saudiyya sun koma gida, saboda tsamin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi.

Kafar yada labaran kasar ta rawaito cewa dukkan jami'an diplomasiyyar 54 da iyalansu sun sauka birnin Tehran.

Tun da farko, shugaba Hassan Rouhani ya ce za a hukunta wadanda suka farwa ofishin jakadancin Saudiyya a kasar a gaban shari'a, a wani yunkuri na kwantar da tarzomar da ta taso.

Ministan harkokin wajen Iraqi Ibrahim al-Jaffari ya ce kasarsa a shirye ta ke ta shiga tsakani dan sasanta rikicin da kasashen biyu ke yi tun bayan da Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan fitaccen malamin Shi'a, Sheikh Nimr al-Nimr.

Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyep Erdogan ya ce zartrar hukuncin kisa da kasar Saudiyya ke yi al'amari ne da ya shafe ta ita kadai.

Kasar Djibouti ta bi sahun kasashen da suka yanke alaka da kasar Iran.