Za mu yi sulhu tsakanin Iran da Saudiyya - Iraki

Hakkin mallakar hoto epa

Ministan harkokin wajen Iraki, Ibrahim al-Jaffari, ya ce a shirye kasarsa take ta yi sulhu a kan takaddamar da ke tsakanin kasashen Iran da Saudiyya.

Mista al-Jaffari ya bayyana haka ne a wajen wani taron hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa na kasar Iran, yana mai cewa idan har aka bar takaddamar ta tsananta, babu wanda zai ji dadi.

Kasar Iraki - wadda mabiya mazhabin Shi'a ke da yawa a cikinta - tana da iyaka da Iran da kuma Saudiyya.

Akwai yiwuwar ci gaban rashin jituwa tsakanin Iran da Saudiyya zai gurguntan harkoki a Iraki, wadda ke fama da rikice-rikicen addini.