Shafin Netflix ya fadada ayyukansa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shafin Netflix da ke bai wa mutane damar kallon bidiyo ta intanet ya ce ya fadada ayyukansa zuwa wasu karin kasashe 130 a duniya.

Kamfanin na Netflix ya ce yana kuma kokarin fadada ayyukan na shi zuwa China, sai dai ya ce ba shi da niyyar gudanar da ayyukan shi a Koriya ta Arewa, da Syria, da Crimea inda dokokin Amurka suka hana shi aiki.

Shugaban kamfanin, Mista Reed Hastings ne ya sanar da hakan a jawabin da ya gabatar a wajen wani taro a Las Vegas.

Darajar hannayen jarin kamfanin ta karu da kashi 8 cikin dari, bayan an bayar da sanarwar.

Wani kwararre daga kamfanin tuntuba kan fasaha na Gartner, Fernando Elizalde ya ce dama suna sa rai shafin na Netflix zai karade ko ina a duniya da ayyukan shi, to sai gashi hakan ya yiwu cikin sauri da basu zata ba.

Sai dai a cewar Mista Fernando, a kasashe masu tasowa, mutanen da suke birane ne kadai za su iya amfani da shafin na Netflix saboda karancin intanet a yankunan karkara.