Za a kafa sansanin sojin sama a Bauchi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin sama suna shiga cikin dajin Sambisa

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na kafa wani katafaren sansanin sojin sama a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.

Kafa wannan sansani na zuwa ne yayin da dakarun tsaron Najeriya da na kasashe makwaftanta, wato Nijar da Kamaru da Chadi ke ci gaba da kokarin murkushe masu tayar da kayar baya na Boko Haram a yankin.

Kawo yanzu dai rundunar ba ta bayyana lokacin da za a kammala aikin gina sabon sansanin ba, a wani wuri da ke wajen birnin Bauchi kan hanyar Kano.

Babban hafsan sojojin sama na Nijeriya Air Marshall Sadique Abubakar -- wanda ya kai wata ziyarar gani da ido a wurin da za a gina sansanin -- ya shaida wa BBC cewa sansanin zai taimaka wajen yaki da Boko Haram.