Mutum 150 sun kamu da zazzabin lassa a Nigeria

Hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun ce an samu bullar zazzabin Lassa a akalla jihohi bakwai a fadin kasar.

Shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC cewa zuwa yanzu kuma kimanin mutum 150 ne suka kamu da ita.

A cewarsa, "Cutar ta bulla ne a jihohi bakwai, wadanda suka hada da Kano da Bauchi da Oyo da Naija da Ribas da Taraba da Nasarawa. Jihohi hudu sun fi kamuwa da cutar".

Ya ce duk da cewa ba a gama tantance yawan wadanda cutar ta hallaka ba, gwamnati na bakin kokarinta wajen ganin an hana yaduwarta a sauran sassan kasar.

Halimar Umar Saleh ta soma da tambayar Farfesa Nasidi jihohin da cutar ta bulla a cikinsu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

<span >