Farashin mai na ci gaba da rigizowa kasa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Faduwar farashin mai na tasiri a kasashe da dama a duniya

Farashin danyan mai a kasuwannin duniya ya fadi da kasa da dala 35 kan kowacce ganga, faduwar da ba a taba gani ba cikin shekaru 11.

Bayan da kasuwarsa ta cushe a duniya, farashin danyen mai nau'in Brent a yanzu kashi daya ne cikin uku na yadda ake sayensa a tsakiyar 2014, duk kuwa da cewa ana zaman dardar a yankin Gabas ta tsakiya.

An yi hasashen cewa takaddamar da ke tsakanin Iran da Saudiyya ka iya janyo farashin man ya tashi.

Maimakon haka sai farashin ya kara faduwa, a sakamakon hasashen da ake yi cewa kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC za ta amince ta rage yawan man da suke hakowa da nufin bunkasa farashinsa.

Maimakon hakan sabanin da kasashen ke ciki ba zai bari su amince a rage yawan man da ake fitarwa ba dan a kara fashinsa.