Kun san abin da ya jawo takkadama tsakanin Saudiyya da Iran?

Hakkin mallakar hoto EPA

Kun san abin da ya jawo takkadama tsakanin Saudiyya da Iran?

Saudiyya ta raba-gari da Iran a harkar diplomasiyya sakamakon kisan fitaccen Malamin Shi'a, Nimr al-Nimr da Saudiyyar ta yi.

Manyan kasashen biyu suna adawa da juna ne kan rigingimu daban-daban da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya.

To amma me ya sa kiyayyar tasu take kamari?

Iran ta ce Saudiyya za ta gamu da fushin Ubangiji saboda kisan da ta yi wa Malamin, kuma masu zanga-zanga a Tehra,n babban birnin Iran sun kona ofishin jakadancin Saudiyya a ranar Lahadi.

Wannan dai ita ce takaddama ta baya-bayan nan da ta sa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyun ta yi tsami.

To amma me ya sa tun a baya kasashen biyu suke adawa da juna?

Ga dai wasu dalilai bakwai da suka jawo takun-saka tsakanin Saudiyya da Iran:

Addini

Babban dalilin da ya jawo wannan kiyayya shi ne kowacce cikin wadannan kasashe na ganin ita ce take kan akidar addinin Musulunci madaidaiciya.

A iya cewa mabiya addinin Musulunci sun kasu gida biyu, da 'yan Sunna da 'yan Shi'a.

Rarrabuwar kawunan dai ta samo asali ne jim kadan bayan wafatin Annabi Muhammad (SAW) kan ko wa ye zai jagoranci al'ummar Musulmai.

Saudiyya dai ita ce take da manyan wurare mafiya tsarki da daraja na Musulunci guda biyu a Makkah da Madina, wanda hakan ya ba ta damar zama jagorar 'yan Sunna a duniya.

Iran ita ce take da mafi yawan mabiya akidar Shi'a a duniya, kuma tun lokacin da aka yi juyin-juya-hali a Iran cikin shekarar 1979 ta zamo ita ce jagorar akidar Shi'a a duniya baki daya.

Siyasar bangaranci

Iran da Saudiyya su ne kasashen da suka fi karfin fada-a-ji a yankin gabas ta tsakiya kuma suna da dakarun tsaro masu karfi.

Kasashen biyu suna kuma gasa wajen ganin sun samu karfin fada-a-ji a kasashen da ke makwabtaka da su, kuma Saudiyya na matukar zargin Iran da yin amfani da karfi cikin al'amuran 'yan tsirarun mabiya Shi'a da ke kasar, da ma wadanda ke kasashen Bahrain da Iraki da Syria da Lebanon.

Shirin nukiliyar Iran da kuma yiwuwar cewa wata rana za ta iya mallakar makaman nukiliya ya tayar da hankalin kasashen da ke makwabtaka da ita musamman ma dai Saudiyya.

Manufofin siyasa

Sarakuna ne ke mulkin kasar Saudiyya kuma suna gudanar da mulkinsu kan tsarin shari'ar Musulunci.

Hakkin mallakar hoto AP

Juyin juya hali na Iran ya fi na Saudiyya tsauri, sannan kuma jagoran juyin juya halin da aka yi a Iran a shekarar 1979, Ayatollah Khomeini, yana ganin tsarin mulkin da ake yi a Saudiyya ba na Musulunci ba ne.

Ana kallon juyin juya halin da ya faru wanda ya kai ga fara mulkin Shi'a a shekarar 1979 a matsayin wata barazana ga mabiya Sunna, musamman ma a kasashen yankin Gulf, kuma dukkan kasasehn Larabawa na zargin Iran tana so ta yi irin wannan juyin juya hali a kasashen da ke makwabtaka da ita.

Iran ta nuna matukar goyon bayanta ga fafutukar da Palasdinu ke yi na neman 'yanci daga wajen Isra'ila, hakan kuma ya sa kasashe mabiya Sunni irin su Saudiyya suka yi ko-oho da kare hakkin Palasdinawa, maimakon haka sai suka dinga kare ra'ayin kasashen yamma.

A tarihince dai, akwai kyakkyawar alaka tsakanin Saudiyya da kasashen yamma, wadanda suke samarwa da Saudiyyan makamai na makudan daloli.

Tun shekarar 1979 dangantakar Iran da kasashen yamma ta baci, kuma hakan yasa kasashen yamma suka sanyawa Iran takunkumin tattalin arziki kan kallon da take mata na mai son mallakar makaman nukiliya.

Syria

Kamar dai Rasha, Iran ta kasance babbar mai goyan bayan shugaban Syria Bashar al-Assad.

Hakkin mallakar hoto AP

Ana tsammanin karfin sojin kasar da kuma abokiyarta kungiyar Hezbollah da ke Labanon, su ne manyan abubuwan da suka sa har yanzu Assad ke kan mulki.

Saudiyya kuwa ita ce babbar mai goyon baya tare da tallafawa kungiyoyin 'yan tawaye masu adawa da gwamnati.

Saudiyya ta kuma yi wani taro domin hada kan kungiyoyin 'yan tawaye da dama don kin jinin gwamnatin Assad.

Iraki

Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf sun goyi bayan Saddam Hussein lokacin yakin da aka yi tsakanin Iran da Iraki daga shekarar 1980 zuwa 1988, sun kuma fuskanci hare-haren Iran .

An dakatar da dangantakar diplomasiyya tsakanin Iran da Saudiyya na tsawon shekaru uku sakamakon wannan yaki.

Hakkin mallakar hoto i

Tun bayan murkushe mulkin Saddam, akasarin mabiya Shia a Iraki suna jagorantar gwamnatin kasar kuma suna da alaka mai karfi da Iran.

Lamarin da ya kawo tasirin Iran a iyakar Saudiyya kuma ya samar da wata gamayyar Iran da Iraqi da Syria da kuma Lebanon.

Baghdaza ta zargi Saudiyya da marawa kungiyoyin Sunni masu tsattsaurar ra'ayin addini baya kuma su ke jawo rikice-rikicen addini a Iraki.

Yemen

Saudiyya da Yemen suna yanki, kuma Yemen na da 'yan kabilar Houthis, mabiyan Shi'a da dama.

'Yan kabilar Houthis sun yi tawaye kuma suka kwace ikon Yemen, ciki har da babban birnin kasar, Sanaa, wanda hakan ya tilastawa magoya bayan gwamnatin Saudiyya gudun hijira a farkon shekarar 2015.

Jihohin daular larabawa da yankin Gulf sun zargi Iran da tallafawa 'yan Houthi da kudi da sojoji, zargin da Iran din ta musanta.

Sa hannun Iran a makwabciyar Saudiyya babban abin damuwa ne a Riyadh, kuma kasashen hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta suna ta fafatawa da 'yan ta'adda.

Mai

Mai na da matukar amfani ga dukkan kasashen - Saudiyya ce kasar da ta fi samar da kuma fitar da mai a duniya - amma ta yiwu suna da bukatu daban-daban a yawan man da take samarwa da kuma farashin da take sayar da shi.

Saudiyya tana da arziki daidai gwargwado kuma yawan mutanen kasarta bai kai na Iran ba.

Ta ce za ta iya jure faduwar da farashin mai ya yi a yanzu na gajeren-zango.

Kasar Iran tana matukar bukatar kudin shiga don haka za ta fi son farashin gangar mai ya karu.