MDD ta soki matakin Korea ta Arewa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Ban ya ce Korea ta Arewa ta wuce gona da iri

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah-wadai da matakin da Korea ta Arewa ta yi na gwajin makamin kare dangi da aka hada da sinadarin Hydrogen.

Korea ta Arewa ta sanar da cewa, ta yi gwajin makamin kare dangi da ta kera cikin nasara, to sai dai kuma wasu kwararru na nuna shakku kan batun gwajin makamin, idan har hakan ta tabbata wannan ya nuna Korea ta Arewa na kokarin fadada makaman nukiliya da take kerawa.

Sakatare Janal na Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon da ya jagoranci taron gaggawa da aka yi a birnin New York ya ya yi Allawadai da gwajin da Arewa ta yi.

Ya ce "Wannan mataki da Korea ta Arewa ta dauka zai kawo rashin tabbas ga zaman lafiya a yankin, kuma zai yi illa ga yarjejeniyar kasa da kasa."

A bangare guda kuma kasashen duniya na kiran a kakabawa Korea ta Arewa takunkumi.