Dabbobin Zimbabwe za su yi gudun hijira

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A kwanakin baya ne aka kashe wani fitaccen zaki a wani gidan ajiye namun dajin Zimbabwe.

Kasar Zimbabwe ta ce za kaurar da wasu dabbobin dajinta zuwa kasar China.

Ministar Muhallin kasar, Oppah Muchinguri ce ta bayyana haka, tana cewa matakin zai taimaka wajen rage mutuwar da dabbobin ke yi sakamakon fari, dabbobin da suka hada da giwaye da ko Gwaggon-birrai, da zakoki da kuraye.

Ta ce kasarta za ta samu wasu na'urori na zamani, musamman jiragen yaki marasa matuka da za a yi amfani da su wajen yaki da barayin dabbobin daji.

Sai dai wasu na sukar wannan mataki na kaurar da dabbobin zuwa kasar Sin, saboda a cewarsu yin haka zai janyo karancinsu a tsakanin al'umomi masu tasowa a kasar.

Mafarauta dai na yin barazana ga gandun dajin Zimbabwe, wadanda ke sayar da hauren giwa da sauran sassan dabobin ga kasashen Asiya, inda ake sarrafa su a matsayin magungunan gargajiya ko kayan kawa na kyauta irin ta alfarma.