Boko Haram: Wadanda suka tsallake rijiya da baya

Fiye da 'yan Najeriya miliyan biyu ne suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin Boko Haram da aka shafe shekaru shida ana fafatawa.

Daya daga cikin sansanonin da ke Maiduguri, shi ne na Dalori wanda aka kafa tantuna da dama.

Abokin aikinmu, Jimeh Saleh ya gana da wadansu daga cikin mutane 18,000 da ke sansanin wadanda Allah ya yi wa gyadar dogo, domin jin yadda rayuwarsu ta kasance.

Mai Mutti

Daya daga cikin mutanen da ke sansanin Dalori, Mai Mutti ya na amfani da sandar guragu.

Mai shekaru 55, tsohon dan kasuwa ne wanda ya tsere daga Bama tare da dubban mutanen da ‘yan Boko Haram suka fatattaka a 2014.

An harbe shi a kafarsa ta hagu, abin da ya sa yake dingishi.

“Ina kwance a kan gado lokacin da suka diran mana da asuba, a lokacin ina jinyar harbi na da aka yi,” in ji Mutti.

‘Yan Boko Haram sun kashe da na dan shekaru 24 sannan suka sace ‘ya’yana mata biyu.

A yanzu yana zaune a Dalori da matansa biyu da ‘ya’ya 10 da kuma jikoki uku.

Fitinar da suka shiga da su da ‘ya’yansu abin ba a cewa komai, amma duk da haka ‘ya’yansu na cikin annashuwa.

Galibin wadanda ke sansanonin ba su kai shekaru 18 ba, wadanda ba sa iya tunawa da abubuwan da suka faru da kuma kalubalen da ke tafe.

Amma kuma akwai yunwa da cutar Malariya da wasu cututtuka na kara yaduwa a sansanin.

“Wannan shi ne abu mafi muni da na taba gani a rayuwa ta,” in ji Noah Bwala malamin asibiti a cikin sansanin.

Ma'aji Modu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Daya daga cikin masu dafa abinci a wannan sansanin sunanta Malama Modu, wacce har yanzu ba ta san makomar mijinta da ‘ya’yanta takwas ba.

An sace wasu daga cikin ‘ya’yanta a gidansu da ke garin Bama sannan ‘yan Boko Haram din suka sace sauran a makaranta.

Tace “Ina kuka duk lokacin da na tuna da su”.

An bata aikin dafa abinci domin kwantar mata da hankali a sansanin.

Ya Ammuna

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Daga cikin dattawa a sansanin akwai Ya Ammuna, mai shekaru 100 da haihuwa.

Tsohowar har yanzu tana cikin bakin ciki saboda ‘yan Boko Haram sun karbe ma ta gidaje biyu a Bama.

Mayakan Boko Haram sun kwace mukullan gidan da karfin bindiga.

Amma har yanzu bata fitar da tsammani ba, saboda sojoji sun kwato garin, kuma za su mayar da ita gida idan an samu zaman lafiya.

Modu Bulama da matarsa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Duk da irin yanayin da ake ciki a sansanin Dalori, wasu sun shiga fagen soyayya.

Modu Bulama mai shekaru 35 ya je sansanin ne bayan da’yan Boko Haram suka kashe matarsa da ‘ya’yansu biyu.

A lokacin da yake aikin bada taimako wajen rarraba kayan agaji a sansanin, sai ya hadu da matarsa, wacce ita ma aka kashe mata miji a rikicin.

Bayan sun ji labaran juna, sai suka amince su yi aure.

Ya biya sadakin dala hamsin kafin su yi auren.