Za a je zagaye na biyu a zaben CAR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Faustin Touadera
Hakkin mallakar hoto .
Image caption Anicet Georges Dologuele

Jami'an zabe a Jamhuriyar tsakiyar Afirka sun ce da alama tsaffin firaministocin kasar biyu, za su je zagaye na biyu na zaben shugaban kasar a karshen watan Janairun nan.

Sakamakon da aka samu na zagayen farko na zaben da a ka yi a watan Disamba, wanda 'yan takara 30 su ka fafata, na nuna cewa zagaye na biyu na zaben za ayi ne tsakanin, Anicet Georges Dologuele da Faustin Archange Touadera.

Ana fatan zaben zai kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi a kasar tsakanin Musulmai da 'yan bindiga kiristoci, inda dubban mutane suka mutu.