Iran ta ce an kai hari a ofishinta da ke Yemen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ofishin jakadancin Iran a Yemen

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya ce, jiragen yakin kasar Saudiyya sun kai hari a kan ofishin jakadancin Iran din da ke Sana'a, babban birnin kasr Yamen.

Sai dai 'yan jarida sun sheda wa BBC cewa su ba su ga wata alama ta kai hari ba.

Kafar labaran Iran din ta ce wasu masu gadi a ofishin jakadancin sun sami raunuka.

Kawancen da Saudiyyar ke jagoranta a yaki a Yeman din ya ce yana bincikawa.

Rahotanni daga Yemen din sun ce an kai hare-hare ta sama da dama da safiyar ranar Alhamis.