Za a sanya wa Koriya Ta Arewa sabon takunkumi

Image caption Wannan shi ne gwajin nukiliya na hudu da kasar ke gudanarwa, amma wannan ne karo na farko da ake gwajin H-Bomb.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba domin sanya wa Koriya ta Arewa sabon takunkumi bayan ikirarin da ta yi na gwajin makamin kare dangi da aka hada da sinadarin Hydrogen.

Shugaban kwamitin tsaron, Mista Elbio Rosselli ya ce ana bukatar daukar karin matakai a kan kasar.

Akwai dai masu shakkar cewar Koriya Ta Arewan ta yi gwajin sinadarin hydrogen ga na'urar, inda masana ke cewa fashewar bam din bai yi karfin sinadarin Hydrogen ba.

Koriya Ta Arewa na fama da takunkumin da aka gindaya mata, duk da haka kuma sakataren harkokin wajen Biritaniya Philip Hammond ya ce akwai yiwuwar za a kara tsaurara takunkumi a kasar.

Wannan shi ne gwajin Nukiliya na hudu da kasar ta yi tun daga shekarar 2006, amma idan an tabbatar da na wannan karon, shi ne zai zamo gwajin H-Bomb na farko da kasar ta yi.