Yaro a Somalia ya kera mota mai amfani da batir

Image caption Motar da Abdi ya kera

Wani yaro dan Somalia mai shekaru 13, Guled Adan Abdi ya kera mota da helikopta da fanka masu amfani da batir.

Yaron wanda ke garin Puntland bai dade da soma karatun makarantar sakandare ba.

Hukumomi a yankin Puntland sun yaba da kokarin Abdi, abin da ya sa gwamnati ta dauki nauyin karatunsa, sannan kuma aka gayyace shi bikin baje koli domin ya nuna bajintarsa a gaban shugaban kasar.

A yanzu haka wannan bajinta ta sa yaron ya samu daukaka a Somalia inda ake maganarsa sosai a shafukan zumunta na zamani.

Image caption Abdi na kokarin nuna fasaharsa