Amurka ta kai wasu fursunoni Ghana

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ta kai wasu fursunoni biyu 'yan kasar Yemen da ake tsare da su a gidan kurkuku na Guantanamo zuwa kasar Ghana.

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce tun a shekarar 2006 aka amince a saki daya daga cikin mutanen, Khalid Dhuby, yayin da mutun na biyun, Mahmoud Omar Bin Atef, aka amince a sake shi a shekarar 2009, da zarar an samu wata kasa da ta nuna za ta karbe su.

Mutanen wadanda ba a taba tuhumarsu da aikata wani laifi ba, ba za a bar su su koma kasarsu Yemen ba.

Su ne kuma fursinonin kurkukun Guantanamo na farko da aka mayar da su yankin yamma da Sahara na nahiyar Afirka.

Firsinonin da suka rage a kurkukun na Guantanamo yanzu, da kadan suka haura dari, kuma kusan rabin su, an amince a mayar da su wasu kasashe.