Ana kammala zaben gwamna a Bayelsa

Image caption A kwanakin baya ne INEC ta soke zaben jihar ta Bayelsa sakamakon rikici da zargin aikata laifukan zabe.

A Najeriya, a yau Asabar ne ake kammala zaben gwamnan jihar Bayelsa, a karamar hukumar Kudancin Ijaw, da kuma wasu mazabu da aka soke zabensu a kananan hukumomi shida na jihar.

Hukumar zaben kasar watau INEC, da kuma rundunar 'yan sandan Najeriya sun ce sun shirya, domin ganin an gudanar da zaben yadda ya kamata.

Ga ma karin bayanin da Kakakin hukumar zabe ta kasa Mista Nick Dazan ya yi wa wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmad:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A kwanan baya ne hukumar ta INEC ta bayyana zaben da aka yi na gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar da cewa bai kammala ba, daga bisani kuma ta soke zaben karamar hukumar Ijaw ta kudu saboda zargin kwace akwatunan zabe da sauran laifukan zabe.