Sabuwar dokar watsa labarai a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Kenyatta da mataimakinsa, William Ruto

Hukumar sadarwa ta Kenya ta wallafa wasu sabbin dokoki na watsa labarai wadanda a ciki ta haramta watsa duk wasu shirye-shirye na batsa da rana a cikin kasar.

Ana jin dai wannan shi ne karo na farko da hukumar ta yi kokarin sanya takunkumi a kan abubuwan da gidajen rediyo na kasar ke watsawa.

Wakiliyar BBC ta ce a wasu lokutta gidajen rediyo masu farin jini a kasar sukan watsa shirye- shirye da suka kunshi batsa a lokacin da mutane suka fi sauraren rediyo domin kiran kasuwa.

Gidajen rediyon kan wasu shirin inda za ka ji wasu iyeye maza suna bayyana sha'awarsu ta tarawa da 'ya'yansu ko kuma wasu mata suna amsa yin kwartanci.

A yanzu dokar ta kayyade irin wadannan shirye shirye tsakanin goma na dare zuwa karfe biyar na safe.

Haka nan kuma dokar ta haramta shirye-shiryen addini, inda ake neman kudi domin samun tabarraki.