Zazzabin Lassa ya kashe mutane 40 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Meyer Rochow and Megu
Image caption Baraye ne ke yada zazzabin Lassa

Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta ce zazzabi Lassa ya hallaka mutane 40 a jihohi goma a fadin kasar.

Ministan Lafiya na kasar, Farfesa Isaac Adewole wanda ya bayyana haka, ya ce hukumomin lafiya na kokari domin shawo kan cutar.

"An samu rahotannin cewa mutane 86 sun kamu da cutar, a yayin da 40 daga ciki suka rasu," in ji Adewole.

Jihohi bakwai ne a arewaci da kuma wasu uku a kudancin kasar aka tabbatar da cutar ta bulla.

Jihohin arewacin su ne Bauchi, Nasarawa, Niger, Taraba, Kano, Plateau da kuma Gombe.

Sai kuma a kudancin kasar, cutar ta bulla ne a jihohin Rivers, Edo da kuma Oyo.

Cutar ta soma bulla ne a jihar Bauchi a watan Nuwamba.

Cutar dai wacce bera ke yada ta, na sa sassasan jiki da dama na jikin dan dan adam su daina aiki.