Ana cin ganye da kasa saboda yunwa a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fatan za ta fara kai daukin kayan abinci daga ranar Litinin a garin Madaya na kasar Syria da aka yi wa kawanya, inda rahotanni ke cewa mutane suna mutuwa saboda yunwa.

Hukumar samar da abinci ta majalisar ta shaida wa BBC cewa manyan motoci dauke da kayan abinci sun shirya tsaf domin zuwa garin, tana mai cewa abin da ake jira kawai shi ne tsara hanyoyin tabbatar da ba a kai musu hari ba idan suka shiga garin wanda ke hannun 'yan tawaye.

A yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin Syria, za kuma a kai daukin wasu kayan abincin kauyukan Foua da Kefraya da su ma aka yi wa kawanya.

Wata da watanni ke nan 'yan tawaye ke kawanya da garin Madaya, kuma likitoci a garin sun ce komai ya kare musu, idan ban da allurar ruwan gishiri da suga da suke yi wa yara domin su ci gaba da rayuwa.

Wasu mutanen garin sun ce dole ta sa sun koma cin ganye da kasa saboda rashin abinci.