Shan giya ba shi da amfani ko kadan'

Hukumomin lafiya a Birititaniya sun ce babu wani adadin giya da ke da amfani.

Babbar shawarar da aka bayar a karon farko cikin shekara 20 a kan batun, ta nuna cewa shan giya ko da kadan ne ka iya yin barazanar kamuwa da cutar daji ko Cancer.

An bayar da shawarar cewa kada maza da mata su rika shan barasa ta wine da yawanta ya wuce kofi 7 ko kuma lita 3 na barasar Beer a mako -- kuma ya zamto an sha yawan barasar a kwanaki daban-daban har tsawon kwanaki uku.

Hakan ya sa Biritaniya ta bi sahun kasashe irinsu Australia da Canada, wadanda da ma can suka gano cewar akwai alaka tsakanin shan barasa da ciwon daji.