Za a sayar da hannun jarin kamfani man Saudiyya

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Aramco shi ne mafi girma a duniya

Kamfanin mai na kasar Saudiyya, watau Saudi Aramco, ya tabbatar da cewar yana yin nazari a kan sayar da hannayen jarin kamfanin ga jama'a.

Kamfanin na Saudi- Aramco, shi ne kamfanin makamashi mafi girma a duniya, inda ya ke da kashi goma cikin dari na yawan man da ake tonowa a duniya.

Wannan sanarwa ta biyo bayan furuncin da Mataimakin Yerima mai jiran gado Saudiyyar, Muhammad Ibn Salman yayi cewar, yana zumudin ganin yiwuwar an sayar da hannayen jarin kamfanin man.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da kasar Saudiyyar take kokarin yin garanbawul a kan harkokin tattalin arzikinta domin maganin wawan gibin da ta samu na kudaden shiga saboda ci gaba da faduwar farashin danyen mai.