Dan IS ya harbe mahaifiyarsa a Raqqa

Hakkin mallakar hoto Islamic State
Image caption Mayakan IS sun ce suna kan bakansu

Masu rajin kare hakkin jama'a a Syria sun ce wani dan kungiyar IS ya kashe mahaifiyarsa a bainar jama'a saboda ta bukace shi ya bar kungiyar.

Bayanai sun ce dan IS din mai suna Ali Sadr dan shekaru 21, ya harbe mahaifiyarsa Lena al-Qasem mai shekaru 45, a kusa da gidan waya da take aiki a birnin Raqqa.

Majiyoyi a Raqqa sun ce mutumin ya bayyana wa mabiyar kungiyar IS cewar mahaifiyarsa ta gargade shi, ya bar kungiyar sannan su gudu saboda dakarun kawance na Amurka za su murkushe kungiyar.

A kan haka ne aka tsare ta, kafin a yanke ma ta hukuncin kisa.

Raqqa ita ce babbar cibiyar kungiyar IS tun a lokacin da suka kwace birnin a watan Agustan 2013.