Hannayen jari sun farfado a China da Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hannayen jari sun yi ta faduwa tu daga farko mako.

Hannayen jarin China da na kasashe Turai sun samu tagomashi a kasuwannin hada-hadar hannayen jari a karon farko, tun bayan da suka yi mummunar faduwa tun daga farkon makon nan.

Sau biyu ana rufe kasuwar hada-hadar hannayen jarin China a wannan makon, ko da ya ke daga bisani an ci gaba da yin hada-hada a kasuwar.

Hannun jari samfurin Shanghai Composite ya tashi da kashi biyu cikin dari ranar Juma'a, sai dai duk da haka ya fadi da kashi goma cikin dari cikin makon.

A London, hannun jari samfurin FTSE 100 ya tashi da maki 21.5, ko kashi 0.36, a kan 5,975.5.

A birnin Frankfurt na Jamus, hannun jari samfurin Dax ya tashi da kashi 0.33, yayin da hannun jarin Cac 40 bai sauya ba a Paris.

A ranar Alhamis, kasuwannin hada-hadar hannayen jarin Turai da Amurka sun yi asara bayan takwararsu ta China ta fada cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa aka rufe ta cikin minti 30.