Jirgin yakin Amurka ya kashe mayakan IS 17

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin yakin Amurka ya hallaka mayakan IS

Wani jami'in Afghanistan ya ce wani jirgin yakin Amurka ya kashe a kalla mayakan kungiyar IS 17, a yankin Nangarhar da ke kasar.

Kungiyar IS tana da runduna mai karfi a wannan yanki.

Gwamnan yankin ya ce wadanda suka mutu din suna shirin fille kawunan wasu mayakan Taliban biyar ne lokacin da jirgin yakin ya kashe su.

Wasu fararen hula biyu kuma sun jikkata.

Har yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba dangane da batun.

Rahotanni daga Pakistan sun ce kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin kungiyoyin masu tayar da kayar bayan biyu, ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 150 a farkon makon nan.