Dickson ya sake lashe zaben Bayelsa

Gwamna Serieke Dickson na jihar Bayelsa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamna Serieke Dickson na jihar Bayelsa

A Najeriya, hukumar zaben kasar ta bayyana dan takarar jam'iyyar PDP, Cif Henry Serieke Dickson a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Bayelsa.

Ya kayar da abokin adawarsa na kut-da-kut Cif Timipreye Silver na jam'iyyar APC.

Babban Baturen zaben jihar, Zana Akpaogu, ya ce Zana Akpaogu, Mista Dickson ya samu kuri'a 134,998 yayin da Timipre Sylva ya samu kuri'a 86,852.

An dai gudanar da karashen zaben ne a karamar hukumar kudancin Ijaw da kuma wasu mazabu da aka soke zabensu a kananan hukumomi shida na jihar.

Rahotanni dai sun ce an samu dan yamutsi a wasu wurare da aka gudanar da zaben a ranar Asabar.