Jami'an tsaro sun kashe mayakan IS a Masar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan kasa Masar

Jami'an tsaro a Masar sun harbe wasu 'yan bindiga biyu da ake zargi 'yan kungiyar IS ne, wadanda suka diran ma wani otal a wurin shakatawa na Hurghada dake kusa da Bahar Maliya.

Rahotanni sun ce bisa dukkan alamu an kaddamar da harin ne domin sace baki masu yawon bude ido.

Wasu turawa 'yan yawon bude ido uku ne suka samu rauni a harin, wanda ya auku bayan 'yan bindigar sun shiga otal din.

Shaidu dai sun ce maharan sun tunkari baki a Otel din ne, inda suka daga musu bakar tutar kungiyar IS.

Wannan shi ne hari na biyu da aka kai kan masu yawon bude ido cikin wasu kwanaki a Masar, inda bangaren yawon bude idonta, ke cikin rudani tun bayan kakkabo jirgin fasinja na Rasha da kungiyar IS ta yi, a watan Nuwamban bara.