Jamus: Za a canza dokar mayar da 'yan cirani gida

Hakkin mallakar hoto AFP

Karkashin dokar ake amfani da ita yanzu, ana iya tasa- keyar masu neman mafaka ta karfin tsiya ne kawai idan har aka yanke masu hukuncin daurin gidan yari na akalla shekaru uku

Sai dai ana tsammanin Jami'ai daga jam'iyyar Shugabar Jamus din za su gabatar da kudurin dokar cewa 'yan ciranin da aka yankewa zaman gidan yari na duk wani lokaci mai tsawo, su fuskanci tasa- keyarsu gida

Wannan shi ne karon farko da shugabar Jamus din ta fito karara ta na goyan bayan canza dokar

A bara ne dai Jamus ta karbi 'yan gudun hijira da kuma 'yan cirani fiye da mutane miliyan daya.

Sai dai bayan hare- haren da aka kai a birnin Colon, hukumomin kasar sun ce, cikin mutane 31 da ake zargi, 18 daga cikinsu masu neman mafaka ne.

Masu kamfe din yaki da 'yan cirani dai sun yi amfani da wannan damar a matsayin wani misali na gazawar wannan manufa ta kasar akan masu neman mafaka. Daruruwan mutane ne ake tsammanin za su yi wata zanga zanga a kan wannan batu a wajen tashar jiragen ruwa ta Colon a yau