Kasashen Gulf na taro kan rikicin Iran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan harkokin wajen Saudiyya Al-Jubeir

Kwamitin hadin kan kasashen yankin Gulf shida na taro a ranar Asabar a Riyadh babban birnin Saudiyya, domin tattauna karuwar tashin hankalin da ake samu tsakanin Saudiyyar da Iran.

A makon da ya gabata ne aka samu tashin-tashina tsakaninn kasashen bayan da Saudiyya ta aiwatar da hukuncin kisa a kan wani fitaccen Malamin Shi'a a kasar.

Kasa daya ce kawai daga cikin kasashen yankin Gulf din ta bi sahun Saudiyya wajen yanke huldar diflomasiyya tsakaninta da Iran.

Amma rahotanni na cewa Saudiyya za ta yi amfani da taron wajen ganin ta gamsar da sauran kasashen yankin don ganin sun bi sahunta wajen yanke huldar diflomasiyya da Iran.

A ranar Juma'a ne ministan harkokin wajen Iran Javed Zarif, ya aike wata wasika zuwa ga sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-Moon, yana zargin Saudiyya da goyon bayan masu tsattaurar ra'ayin addini, da kuma shiga yaki ba gaira ba dalili a kasar Yemen.