Mexico: Guzman ya sake shiga hannu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Guzman ya taba tserewa daga Gidan Yari a baya

Hukumomi a Mexico sun sake kama wani madugun hada-hadar miyagun kwayoyi a kasar, Joaquin "El Chapo" da aka fi sani da Guzman, watanni shida bayan ya tsere daga wani babban gidan kurkuku.

An kama shi ne bayan musayar wuta da jami'an tsaro a birnin Mochis na jihar Sinaloa.

Sojojin ruwa na Mexicon ne suka jagorancin farautar sake kamashi.

Sake kamashin da aka yi kuma, ya biyo bayan doguwar farautar mutumin ne, wanda a karo na biyu, ya kunyatar da hukumomin kasar ta hanyar tserewa daga kurkuku.

Guzman dai hamshakin maikudi ne, kuma mujallar Fobes ta bayyana shi a matsayin daya daga cikin masu kudi