An tantance Hama Amadou a Nijar

Hama Amadou Hakkin mallakar hoto
Image caption Dan takarar shugaban kasar Nijar

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijar -CENI ta tantance Hama Amadou, a matsayin dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar Jama'iyarsa ta Lumana Afrika, duk kuwa da cewar har yanzu yana tsare a kurkuku bisa zargin yana da hannu a safarar kananan yara.

Hama Amadou dai ya musanta wannan zargi, inda ya ce yana da nasaba da siyasa.

Hama Amadou wanda tsohon shugaban majalisar dokoki ta kasar ne na daga cikin yan takara 15 da hukumar zaben ta sahale wa yin takara.

Seidu Bukari, wani jigo ne a jam'iyyar Modem Lumana ta Hamma Amadou, kuma ya bayyana wa Baro Arzika yada suka ji da matakin kotun:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaban kasar mai mulki Mahamadou Issoufou ma zai sake takara a karo na biyu.

A ranar Litinin ne za a yanke shawarar ko za a saki Amadou daga kurkuku.

A cikin wata mai tsayawa ne dai za a yi babban zaben na Jamhuriyar Nijar.