Kotu ta amince da 'yan takara 15 a Niger

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Niger kotun tsarin mulki ta kasar ta amince da 'yan takara goma sha biyar wadanda za su fafata a zaben shugaban kasar a watan gobe.

Daga cikin mutanen da kotun tsarin mulkin ta amince da takarasu har da wani jigon dan adawa Hama Amadou wanda aka tsare a gidan yari watanni biyu da suka wuce bayan da koma kasa daga gudun hijirar da ya yi ta tsawon shekara daya.

Akwai alamun cewa kotun tsarin mulkin za ta matsawa gwamnatin Niger din ta sako Hama Amadou wanda ake gani yana daya daga cikin manyan yan takara uku da za su yi tasiri a gwagwarmayar neman shugabancin kasar ta yammacin Afirka mai arzikin Uranium a zaben na ranar 21 ga watan Fabrairu.

Hukumomin Niger din dai sun kama Hama Amadou tsohon shugaban majalisar dokoki a watan Nuwamba dangane da wani bincike na wasu manyan mutane da ake zargi da safarar jarirai daga Najeriya.

Hama Amadoun ya baiyana zarge zargen a matsayin bita da kullin siyasa