MDD na shirin kai daukin abinci a Madaya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jerin gwanon motocin kayan agaji na iya kama hanyar zuwa garin Madaya a Syria inda aka bada rahoton mutane suna mutuwa saboda yunwa.

Kungiyar Red Cross ta duniya da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya suna shirin tsara tafiyar jerin gwanon motocin dauke da kayan abinci da magunguna da za su wadatar da jama'a kusan dubu arba'in tsawon wata guda.

Mutanen dai sun makale ne a yankin yan tawaye a garin Madaya da ke kusa da kan iyaka da kasar Lebanon.

Ana shirin gudanar da makamancin wannan tsarin a ranar litinin ga wasu kauyuka biyu da ke karkashin gwamnati wadanda kuma yan tawaye suka yiwa kawanya daga arewa maso yammacin gundumar Idlib.

Matakin na zuwa ne yayin da jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura ya isa Damascus domin tattauna shirin sulhun tsakanin gwamnati da yan kungiyoyin adawa da za'a gudanar nan gaba a cikin wannan watan.