Angilika: daidaita matsayi kan luwadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron manyan limaman Angilika

A yau ne shugabannin Kirista mabiya darikar Angilika ke wani taro a Birtaniya da nufin tunkurar wasu manyan batutuwa da suka shafi bambance-bambancen da ke tsakaninsu, musamman batun jinsi da Luwadi.

Da wuya dai watakila su daidaita, ganin cewa masu ra'ayin sassauci a tsakaninsu sun amince da nada 'yan Luwadi a matsayin Limamai, yayin da masu tsaurin ra'ayi, galibi daga nahiyar Afirka ke kyamar Luwadi, suke kuma nisanta kansu da shi.

Wakilin BBC ya ce hada wadannan bangarori a wuri guda na da hadari, kuma watakila wasu su fice daga zauren taron, lamarin da ka iya zama barazana ga makomar Majami'ar Angilikar.