Dickson ya lashe zaben gwamnan Bayelsa

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Seriake Dickson ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa

Hukumar zaben Nigeria ta sanar da Dan takarar Jam'iyyar PDP Seriake Dickson a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Shi dai Seriake Dickson wanda shi ne gwamna mai ci ya samu kuri'u 134,998 yayin da Timipre Sylva na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 86,852.

An dai yi zaben ne bayan da zaben farko na ranar 5 ga watan Disamban 2015 bai samar da wanda ya samu nasara ba.

Hukumar zabe ta gudanar da sauran zaben ne a wasu kananan hukumomi da suka hada da karamar hukumar Yenagoa da Brass da Sagbama da Ogbia da kuma karamar hukumar Kudancin Ijaw.