Motar rusau ta afka cikin wani asibiti a China

Hakkin mallakar hoto REUTERS

Gidan Talabijin na gwamnatin China ya ce an sallami wani jami'in gwamnati wanda ya ke sa ido a kan wani aikin rusau a garin Zhenghzhou bayan ya yi sakacin barin wata motar rusau kutsawa cikin wani asibiti

Likitoci da kuma marasa lafiya dake kwance a asibitin sun ranta- ana- kare, sannan kuma an ruwaito cewa baraguzan ginin asibitin sun binne gawarwakin mutanen dake asibitin

Wannan lamari dai ya faru ne a ranar Alhamis.

An zargi Jami'an birnin da saba ka'idar aiki.

A yanzu haka dai 'yan sanda na gudanar da bincike