An yi zanga zangar bacewar mutane a Hong Kong

Masu Zanga zanga a Hong Kong Hakkin mallakar hoto Reuters

Dubban mutane sun gudanar da wata zanga zanga a Hong Kong domin bayyana fushin da suke ci gaba da shi game da bacewar wasu mutane 5 masu sayar da littattafai da ake jin suna tsare a China.

Ana danganta dukanin mutanen biyar da kanti guda na sayar da littattafai a Hong Kong wanda ke sayar da wallafe - wallafen dake yin suka a kan gwamnatin China.

Mutane 3 sun bata a China, daya ya bace a Thailand sannan na biyar din ya bace yayin da yake ziyartar wata adanarsa dake a Hong Kong.

Masu zanga zangar -- wadanda suka yi maci zuwa Ofishin Gwamnatin China a Hong Kong -- na jin tsoron cewar China na kokari ne na yin makarkashiya ga yanci na musamman da yankin yake da shi, wanda aka tabbatar masa a lokacin da Birtaniya ta mika shi ga Chinar.