Makami mai linzami ya fadawa asibitin MSF

Medecins Sans Frontieres Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ba wannan ne karon farko da ake kai hari kan asibitocin kungiyar ba.

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa Medecins Sans Frontieres ta ce wani makami mai linzami da aka harba asibitinta da ke Yemen ya hallaka akalla mutane hudu.

Asibitin ya na kudancin gundumar Saada ne, inda 'yan tawaye na kabilar Houthi da ke yaki da gwamnatin Yemen da kawayenta irinsu Saudiyya, ke da gagarumin jinyaje a yankin.

MSF tace ba za ta iya tantance ko jirgin yakin kawance da Saudiyya ke jagoranta ne ya kai harin ba, ko kuma makamin roka aka harba.

Shekara guda kenan da mayakan kabilar Houthi su ka karbe iko da babban birnin kasar Yemen wato Sanaa.

Sun kuma ci gaba da fadada kai hare-hare a sassan kasar, duk da kokarin da dakarun gwamnatin Yemen da kawayenta ke yi dan fatattakarsu daga birnin.