Syria: Ayarin MDD zai kai abinci Madaya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yunwa ta halaka mutanen Madaya

Majalisar Dinkin duniya ta ce a yau din nan ne ake sa ran wani ayarin jami'anta dauke da abinci da magunguna zai kama hanyar zuwa garin Madaya da aka yi wa kawanya a Syria.

Rahotanni na cewa kimanin mutum dubu Arba'in ne aka yi wa kawanya a garin sakamakon rufin-gangar da sojojin gwamnatin Syriar suka yi wa garin, kuma ba sake shigar da abincin garin ba tun watan Oktoban da ya wuce.

Majalisar dinkin duniyar ta ce ta samu labarin cewa akwai mutanen da yunwa ta kashe a garin.

A makon jiya ne gwamnatin Syria ta amince za ta kyale ayarin majalisar dinkin duniyar ya shiga garin.

Haka kuma za a kai kayan agajin ga wasu garuruwa biyu da 'yan tawaye suka yi wa zobe a lardin Idlib