Al-Nusra ta sace 'yan jarida a Syria

Mayakan kungiyar Nusra a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Syria sun ce kungiyar dake da alaka da Al-Qa'ida ta yan gwagwarmayar Nusra ta yiwa wani gidan rediyo dirar mikiya, suka yi awon gaba da wasu fitattun 'yan jarida masu fafutika.

Mutanen 2, Raed Fares da Hadi al-Abdallah an dauke su ne daga ofisoshin wani gidan Rediyo da ake kira Fresh FM a garin Kafranbel na arewa maso yammacin kasar wanda 'yan tawaye ke rike da shi.

Kawo yanzu 'yan gwagwarmayar ba su yi cikakken bayani a kan abinda ya sa suka yi hakan ba.

To amma wata kungiyar yan adawar ta bayyana cewar daya daga cikin dalilan shi ne cewar kungiyar masu kishin Islaman mai ra'ayin yan mazan jiya ainun ta Nusra tana adawa da yadda gidan rediyon ke shirye shiryensa tare da tsunduma cikin harkokin addini ba.