Karancin mai ya sake kunno kai a Kaduna

Karancin man fetur ya sake kunno kai a jihar Kaduna da kuma wasu sassan arewacin Najeriya.

Bayanai sun nuna cewa yawancin gidajen mai na gwamnati da na manyan 'yan kasuwa da ke sayar da man fetur a kan farashin gwamnati, ba suda man, abin da ke sa kalilan daga cikin gidajen man ke sayarwa a tsawwalallen farashi.

Dillalan man fetur a Kaduna, na zargin cewa karancin man fetur din ya sake dawowa ne sakamakon son zuciya wajen raba man fetur da hukumar PPMC ke yi.

Wani mai kwarmata bayanai ya shaidawa BBC cewa wasu manyan jamiai a hukumar ta PPMC masu raba mai da gangan sun boye man da matatar mai ta Kaduna ta tura musu.

Bayanan da muka tattaro daga jihar Kano ma sun nuna cewa ana fama da karancin man fetur, inda har yanzu za ka ga layukan motoci a gidajen sayar da man.

Sai dai hukumar ta PPMC ta musanta wannan zargin, inda ta ce tana ci gaba da rarraba albarkatun man fetur a sassa daban-daban na kasar.

Ana yawan fuskantar karancin man fetur a Najeriya saboda matatun man da ke kasar ba sa iya tace adadin man da ake bukata, a don haka dole ne sai an shigo da tattaccen mai daga kasashen waje.