Jafaru Isa ya mayar da naira miliyan 100

Hakkin mallakar hoto DAILY TRUST NIGERIA
Image caption Lawal Jafaru Isa makusancin Shugaba Buhari ne.

A Najeriya, rahotanni na cewa tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Lawal Jafaru Isa ya mayar da Naira Miliyan 100 ga EFCC, da ake zargin tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki ya ba shi.

Wani makusancin Jafaru Isa ya tabbatarwa BBC cewa an mika kudin ne ga hukumar EFCC.

A makon jiya ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, EFCC, ta kama Lawal Jafaru Isa.

Ana tuhumarsa da karbar wani kaso daga cikin dala biliyan biyu na sayen makamai, zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.

Jafaru Isa shi ne mutum na farko a makusantan Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar EFCC ta kama kan zargin badakalar cin hanci da rashawa.